NAZARIN YADDA MARUBUTA KAGAGGUN LABARAI SUKE AMFANI DA ALJANU DOMIN CIMMA MANUFOFINSU NA WALLAFA
Abstract
Wannan bincike ya yi nazarin yadda marubutan ƙagaggun labaran Hausa suke amfani da aljanu a matsayin dabarar adabi domin cim ma manufofinsu na wallafa. An duba yadda ake amfani da aljanu wajen gwada jarumai da isar da saƙo cikin sauri da taƙaita ko tsawaita labari da taimakon taurari da gina salo da tsoratarwa da kuma bayyana siffofi da halayen aljanu. An gudanar da binciken ne ta hanyar nazarin wasu zaɓaɓɓun ƙagaggun labarai kamar Ruwan Bagaja da Magana Jari Ce da Ganɗoki da Aljani Ya Taka Wuta, tare da amfani da ra’in qyallaro al’ada (Referential Theory of Culture). Sakamakon binciken ya nuna cewa amfani da aljanu wata dabara ce ta fasaha da marubuta suke amfani da ita domin sauƙaƙa warware matsalolin labari da gina salo da kuma jan hankalin masu karatu. Binciken ya kuma tabbatar da cewa aljanu sun kasance muhimmin ginshiƙi a adabin Hausa tun daga tatsuniyoyi har zuwa ƙagaggun labarai na zamani.
Downloads
Downloads
Published
Issue
Section
License

This work is licensed under a Creative Commons Attribution-NonCommercial 4.0 International License.
