Kara Bibiyar Salon Iktibasi a Wakar Bidi’a ta Malam Sa’adu Zungur
Abstract
Wannan takarda ta qunshi bayanin yadda Malam Sa’du Zungur ya sarrafa nassi a cikin Waqar Bidi’a. Manufar takardar ita ce qara bibiyar nassi da fito da shi a cikin Waqar Bidi’a biyo bayan binciken Mainasara (2018). A wajen gudanar wannan takarda an qara nazartar Waqar Bidi’a kamar yadda ta zo a cikin Abdulqadir (1974) da kuma Yakubu (1999). Haka nan an xora wannan takarda a kan hanyar nazarin nassi kamar yadda masana suka kawo. Wannan takarda ta yi nasarar gano qarin wasu nassoshi da aka yi amfani da su a cikin Waqar Bidi’a qari ga waxanda Mainasara (2018) ya gano. Dangane da tsakuren nassi guda uku (3) da aka gano a binciken Mainasara (2018), wannan takarda ta kuma gano qarin baitoci uku masu qunshe da tsakuren nassi. Dangane da fassarar nassi guda huxu (4) da Mainasara (2018) ya gano, wannan takarda ta kuma gano qarin guda uku (3). Game da abin da ya shafi ishara zuwa ga nassi, wannan takarda ta kuma gano qarin misali xaya qari ga na Mainasara (2018) guda uku (3).
Downloads
Downloads
Published
Issue
Section
License

This work is licensed under a Creative Commons Attribution-NonCommercial 4.0 International License.
