NAZARIN JIGOGI DA SALON WASU MARUBUTA KAGAGGUN LABARAI NA KARNI NA ASHIRIN DA DAYA (21)

Authors

  • Lawal Adams Kano State College of Education And Preliminary Studies Author
  • Hauwa Muhammad Maikudi Kano State College of Education And Preliminary Studies Author
  • Bashir Shehu Ibrahim Kano State College of Education And Preliminary Studies Author

Keywords:

Salo, Jigogi, Marubuta, Kagaggun Labarai, Karni, Ashirin Da Daya

Abstract

An yi wannan nazari ne a kan yadda tunanin marubuta qagaggun labarai a qarni na 21 ya canza salo yadda ya sha bamban da na qarni na 19 da kuma qarni na 20. Marubuta qagaggun labarai a qarni na 19 sun fi mayar da hankali ne wajen yin rubuce-rubuce a kan abubuwan da suka shafi addini da nasiha da jan hankali da bin dokokin ibada da sauransu. A qarni na 20 kuwa marubuta da yawa sun qaru kuma suka zo da sabon salon rubutu wanda ya bambanta da qarni na 19. A wannan qarni na 20 marubuta qagaggun labarai sun fi mayar da salon rubutunsu a kan abubuwan da suka shafi tarbiyya da tsafta da koya magana da mu’amala da auren dole da saka yara a makaranta, da sauransu. A wannan qarni aka samu jigon da ake kira ‚Baduniyen Jigo‛. A qarni na 21 rubuce-rubucen qagaggun labarai ya sake canza salo wanda ya zarta na qarni na 20. Wannan takarda za ta yi nazari ne kan yadda jigon ya canza salo tare da kawo misalai daga labaran litattafai da kuma labaran ake sanyawa ta gasa da kuma litattafan Adabin Kasuwar Kano. An kuma kawo wasu labaran da suka yi nasara a gasar gidauniyar Arc.Ahmed Musa Xangiwa 2022. An yi qoqarin yin bitar ayyukan da suka gabata wanda suka haxa da ma’anar jigo salo. An yi amfani da hanyoyin da suka haxa da karance-karance da sauraren da ziyartar xakuna karatu wanda suka ba da ikon tattara bayanai. An xora wannan nazari kan Ra’in Mukhtar (2004). An yi qoqarin kawo sakamakon nazarin da kammalawa. 

Downloads

Download data is not yet available.

Downloads

Published

2026-01-20

How to Cite

NAZARIN JIGOGI DA SALON WASU MARUBUTA KAGAGGUN LABARAI NA KARNI NA ASHIRIN DA DAYA (21). (2026). RUMFA Journal of Arts, 4(2), 186-197. https://rumfa.org.ng/index.php/ja/article/view/13