NAZARIN YADDA MARUBUTA KAGAGGUN LABARAI SUKE AMFANI DA ALJANU DOMIN CIMMA MANUFOFINSU NA WALLAFA

المؤلفون

  • Mustapha Kallamu School of Continuing Education Bayero University, Kano Dept. of Arts and Humanities Author

الملخص

Wannan bincike ya yi nazarin yadda marubutan ƙagaggun labaran Hausa suke amfani da aljanu a matsayin dabarar adabi domin cim ma manufofinsu na wallafa. An duba yadda ake amfani da aljanu wajen gwada jarumai da isar da saƙo cikin sauri da taƙaita ko tsawaita labari da taimakon taurari da gina salo da tsoratarwa da kuma bayyana siffofi da halayen aljanu. An gudanar da binciken ne ta hanyar nazarin wasu zaɓaɓɓun ƙagaggun labarai kamar Ruwan Bagaja da Magana Jari Ce da Ganɗoki da Aljani Ya Taka Wuta, tare da amfani da ra’in qyallaro al’ada (Referential Theory of Culture). Sakamakon binciken ya nuna cewa amfani da aljanu wata dabara ce ta fasaha da marubuta suke amfani da ita domin sauƙaƙa warware matsalolin labari da gina salo da kuma jan hankalin masu karatu. Binciken ya kuma tabbatar da cewa aljanu sun kasance muhimmin ginshiƙi a adabin Hausa tun daga tatsuniyoyi har zuwa ƙagaggun labarai na zamani. 

التنزيلات

تنزيل البيانات ليس متاحًا بعد.

التنزيلات

منشور

2026-01-21

كيفية الاقتباس

NAZARIN YADDA MARUBUTA KAGAGGUN LABARAI SUKE AMFANI DA ALJANU DOMIN CIMMA MANUFOFINSU NA WALLAFA. (2026). RUMFA Journal of Arts, 4(2), 198-207. https://rumfa.org.ng/index.php/ja/article/view/14